Joshua 10:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَكُمَ بَادَ وَنَّنْ بِرْنِ دَ سَرْكِنْتَ أَ حَنُّنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا؞ سُكَ كَشٜىٰ كُواْوَنٜىٰ مُتُمِنْ دَيَكٜىٰ ثِكِنْتَ دَ تَكُواْبِے، بَسُ ضَغٜىٰ كُواْ طَيَبَ؞ يُواْشُوَ كُوَ يَيِ وَسَرْكِنْتَ كَمَرْ يَدَّ يَيِ وَسَرْكِنْ يٜىٰرِكُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.