Joshua 11:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَوَنَّنْ لُواْكَثِ يُواْشُوَ يَتَڢِے يَهَلَّكَ یَیَنْ أَنَكْ دَغَ يَنْكِنْ تُدَّيْ دَغَ هٜىٰبْرُوانْ دَ دٜىٰبِرْ دَ أَنَبْ دَ دُكَنْ يَنْكِنْ تُدَّيْ نَ يَهُودَ دَ كُمَ دَغَ دُكَنْ يَنْكِنْ تُدَّيْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ يُواْشُوَ كُوَ يَهَلَّكَرْ دَسُو غَبَاطَيَ دُكْ دَ بِرَنٜىٰنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra'ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu.