Joshua 11:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ وَ يُواْشُوَ «كَدَ كَجِڟُواْرُوانْسُ، غَمَا كَاڢِنْ غُواْبٜىٰ وَرْهَكَ نِے يَهْوٜىٰهْ ذَنْ كَكَّشٜىٰسُ، إِنْ بَادَسُو دُكَ غَ حَنُّنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا؞ ذَاكُ غُرْغُنْتَ دَوَكِنْسُ كُكُمَ ڧُواْنٜىٰ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.”