Joshua 14:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
(Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ دَا أَنَ كِرَنْ هٜىٰبْرُوانْ دَ سُونَ كِرِيَتْ أَرْبَ؞ وَنَّنْ أَرْبَ كُوَ وَنِ ڧَتُوانْ مُتُمْ نٜىٰ عَثِكِنْ أَنَكَاوَا؞ ڧَسَرْ كُوَ تَسَامِ هُوتُ دَغَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.