Joshua 15:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim).
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ كَنْ تُدُنْ إِيَاكَرْ تَمِيڧٜىٰ ذُوَا مَٻُٻُّغَرْ ضُوً نٜىٰڢْتُواْوَ دَغَ ثَنْ تَڢِتَ ذُوَا غَرُرُوَ كُسَدَ بَبَّنْ تُدُنْ عٜىٰڢْرُوانْ، سَيْ تَجُويَا ذُوَا بَعَلَ، وَتُواْ كِرِيَتْ يٜىٰيَرِمْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim.