Joshua 17:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma har da ƙasar kan tudu ma, ko da yake jeji ne, ku je ku gyara shi, duk yă zama naku. Ko da yake Kan’aniyawa suna da kekunan yaƙi na ƙarfe, suna kuma da ƙarfi, duk da haka za ku kore su.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يَنْكِنْ تُدَّيْ مَيْ كُرْمِ ذَيْ كُمَ ذَمَ نَاكُ؞ سَيْ كُسَارٜىٰ كُشَرٜىٰ كُمَلَّكِ يَنْكِنْ دُكَ حَرْ إِيَاكَرْسَ؞ غَمٜىٰ دَ كَنْعَنِيَاوَا كُوَ، ذَاكُ كُواْرٜىٰسُ، كُواْدَيَكٜىٰ سُو مَاسُ ڧَرْڢِے نٜىٰ سُنَ كُمَ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِ نَڧَرْڢٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan'aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”