Joshua 17:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ظٜىٰلُواْڢٜىٰهَدْ طَنْ هٜىٰڢٜىٰرْ جِيكَنْ غِلٜىٰيَدْ طَنْ مَكِرْ نَظُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ كُوَ بَ شِ دَ یَیَ مَظَا، عَمَّا یَیَ مَتَ كَطَيْ يَكٜىٰدَسُو؞ سُونَيٜىٰنْ یَیَنْسَ مَاتَا سُونٜىٰ مَلَ دَ نُواْوَ دَ هُواغْلَ دَ مِلْكَ دَ كُمَ تِرْظَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.