Joshua 17:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “ Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ تَڢِے وُرِنْ عٜىٰلٜىٰيَظَرْ ڢِرِسْتِ دَ يُواْشُوَ طَنْ نُنْ دَ شُوغَبَنِّنْ سُكَثٜىٰ «يَهْوٜىٰهْ يَا عُمَرْثِ مُوسَٰى يَبَامُ رَبُوانْ غَادُوانْمُ، كَمَرْ يَدَّ عَكَبَا یَنْعُوَنْمُ مَظَا؞» يُواْشُوَ كُوَ يَيِ كَمَرْ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْتَ، يَبَاسُ يَنْكِنْ ڧَسَرْ مَلَّكَرْسُ تَغَادُواْ، يَدَّ عَكَبَا یَنْعُوَنْ بَابَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.