Joshua 17:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِيَاكَرْ تَغَنْغَرَ كُدُ ذُوَا رَاڢِنْ كَنَ؞ غَرُضُوً دَسُكٜىٰ عَكُدَنْثِنْ رَاڢِنْ نَ إِڢْرَيِمْ نٜىٰ، كُواْدَيَكٜىٰ سُنَ ثِكِنْ يَنْكِنْ مَنَسّٜىٰ؞ إِيَاكَرْ مَنَسّٜىٰ كُوَ تَبِے غٜىٰڢٜىٰنْ أَرٜىٰوَثِنْ رَاڢِنْ تَكُمَ ڧَارٜىٰ عَتٜىٰكُنْ مٜىٰدِتٜىٰرٜىٰنِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum.