Joshua 18:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِيَاكَرْ تَغَنْغَرَ ذُوَا غِنْدِنْ تُدُ وَنْدَ يَكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ ݣُورِنْ هِنُّوامْ، وَنْدَ يَكٜىٰ أَرٜىٰوَ وَجٜىٰنْ ݣُورِنْ رٜىٰڢَيَاوَا؞ تَا كُمَ غَنْغَرَ ذُوَا ݣُورِنْ هِنُّوامْ تَبِے تَكُدُ دَ بِرْنِنْ يٜىٰبُسِيَاوَا تَمِيڧٜىٰ ذُوَا عٜىٰنْرُواْغٜىٰلْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel.