Joshua 18:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku ba da mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su zagaya dukan ƙasar su rubuta bayani game da ita, bisa ga yadda za a raba ta gādo ga kowace kabila, sa’an nan su dawo wurina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُبَا نِے مُتُمْ عُكُ دَغَ ثِكِنْ كُواْوَثٜىٰ ذُرِيَ؞ نِے كُوَ ذَنْعَيْكٜىٰسُ، سُذَاغَيَ دُكَنْ ڧَسَرْ سُعَوْنَ يَدَّ ذَاعَ رَبَ رَبُوانْ غَادُوانْ ڧَسَرْ بِسَ كُواْوَثٜىٰ ذُرِيَ، سَعَنً سُكُواْمَ وُرِينَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina.