Joshua 18:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da mutanen za su kama hanya su je su zāna yadda ƙasar take, Yoshuwa ya umarce su cewa, “Ku je ku ga yadda ƙasar take. Sa’an nan ku dawo wurina, zan yi muku ƙuri’a a nan Shilo a gaban Ubangiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ كُوَ سُكَتَاشِ سُكَ تَڢِے دُواْمِنْ سُعَوْنَ ڧَسَرْ، بَايَنْ يُواْشُوَ يَبَاسُ عُمَرْنِ ثٜىٰوَ «كُتَڢِے كُذَاغَيَ ثِكِنْ دُكَنْ ڧَسَرْ؞ كُعَوْنَتَ كُرُبُوتَ بَيَانِنْتَ كُكُواْمَ وُرِينَ؞ سَعَنً نِے ذَنْ جٜىٰڢَ مُكُ ڧُرِعَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ أَنَنْ شِلُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.”