Joshua 18:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen kuwa suka tafi suka bi ta cikin ƙasar, suka bayyana yadda take a rubuce, gari-gari, kashi bakwai, suka koma wurin Yoshuwa a Shilo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتَنٜىٰنْ سُكَ تَڢِے سُكَ ذَاغَيَ ڧَسَرْ دُكَ؞ سُكَ رُبُوتَ بَيَانِنْ أَ نَطَطّٜىٰنْ لِتَّڢِ يَدَّ سُكَ رَبَ ڧَسَرْ كَشِ بَݣَويْ، سُكَيِ لِسَّڢِنْ غَرُضُوً دَسُكٜىٰ ثِكِ؞ سَيْ سُكَ كُواْمَ وُرِنْ يُواْشُوَ عَثِكِنْ سَنْسَنِ أَ شِلُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo.