Joshua 2:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ شِينٜىٰ أَبِنْدَ ذَاكِيِ سَعَدَّ مُكَ شِغُواْ ڧَسَرْ؞ سَيْ كِطَوْرَ وَنَّنْ جَرْ إِغِيَ عَتَغَرْ دَ مُكَ سَوْكَ؞ كِكَٰوُاْ بَابَنْكِ دَ مَامَرْكِ دَ یَنْعُوَنْكِ دَ كُمَ دُكَنْ عِيَلَنْسُ أَغِدَنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki.