Joshua 2:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
رَهَبْ كُوَ تَيَرْدَ دَ مَغَنَرْسُ؞ سَيْ تَسَلَّمٜىٰسُ، سُكَ تَڢِے؞ سَعَدَّ سُكَ تَڢِے، تَجٜىٰ تَطَوْرَ جَرْ إِغِيَ عَتَغَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta ce, “Bisa ga maganarku ya zama haka.” Sa'an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar.