Joshua 2:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutanen garin suka kama hanyar Urdun don su nemi ’yan leƙen asirin, daga fitar su sai aka rufe ƙofar garin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَظَرَرْ مُتَنٜىٰنْ سَرْكِنْ سُكَ ڢِتَ دَغَ بِرْنِنْ دُواْمِنْ نٜىٰمَنْ مَاسُ لٜىٰڧٜىٰنْ أَسِيرِنَّنْ، سَيْ عَكَ كُلّٜىٰ ڧُواْڢَرْ؞ مُتَنٜىٰنَّنْ سُكَبِے مَاسُ لٜىٰڧٜىٰنْ أَسِيرِنْ حَرْ ذُوَا عِنْدَ حَنْيَرْ تَكَيْ وُرِنْ دَ عَكٜىٰ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.