Joshua 22:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ عَيْكِ ڢِنٜىٰهَسْ طَنْ عٜىٰلٜىٰيَظَرْ ڢِرِسْتِ وُرِنْ مُتَنٜىٰنْ ذُرِيَرْ رَعُبَيْنُ دَ ذُرِيَرْ غَدْ دَ رَبِنْ ذُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ عَثِكِنْ ڧَسَرْ غِلٜىٰيَدْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.