Joshua 22:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’ ’Ya’yanku za su iya sa ’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا يَهْوٜىٰهْ يَا سَا كُواْغِنْ يُواْدَنْ يَا ذَمَ إِيَاكَ ڟَكَانِنْمُ دَكُو، يَا كُو مُتَنٜىٰنْ رَعُبَيْنُ دَ مُتَنٜىٰنْ غَدْ؞ دُواْمِنْ حَكَ بَاكُ دَ رَبُواْ عَثِكِنْ يَهْوٜىٰهْ ؞› تَهَكَ یَیَنْكُ ذَاسُ حَنَ یَیَنْمُ يِوَ يَهْوٜىٰهْ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada.