Joshua 22:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko ’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba don ƙona hadayu da kuma yin sadaka ba, sai dai don yă zama shaida tsakaninmu da ku.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُنْيِ تُنَانِ ثٜىٰوَ عِدَنْ وَتَرَانَ عَكَ ڢَطَا مَنَ كُواْ كُوَ عَكَ ڢَطَا وَیَیَنْمُ حَكَ، سَيْمُثٜىٰ، ‹كُدُوبِے بَغَدٜىٰنْ دَ كَاكَنِّنْمُ سُكَ غِنَا؞ يَنَنً دَيْدَيْ دَ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ بَسُيِشِ دُواْمِنْ مِيڧَ هَدَايُ كُواْ دُواْمِنْ ڧُواْنَ هَدَايُبَ، عَمَّا دُواْمِنْ شَيْدَ ڟَكَانِنْمُ دَكُو؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’