Joshua 22:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً ڢِنٜىٰهَسْ طَنْ عٜىٰلٜىٰيَظَرْ ڢِرِسْتِ دَ شُوغَبَنِّنْ سُكَ بَرْ مُتَنٜىٰنْ رَعُبَيْنُ دَ غَدْ عَڧَسَرْ غِلٜىٰيَدْ، سُكَ كُواْمَ ڧَسَرْ كَنْعَنَ سُكَ كَيْ وَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا رَهُواْتُوانْ أَبِنْدَ سُكَجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra'ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mutanen Isra'ila, suka ba su rahoton abin da suka ji.