Joshua 22:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُوَ سُكَجِ دَاطِنْ رَهُواْتُوانْ، سُكَ يَبِے اللَّهْ ؞ بَسُ سَاكٜىٰيِنْ ذَنْثٜىٰنْ ذُوَا يَاڧِ دُواْمِنْ سُهَلَّكَ ڧَسَرْدَ مُتَنٜىٰنْ رَعُبَيْنُ دَ مُتَنٜىٰنْ غَدْ سُكٜىٰ ذَمَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba.