Joshua 22:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
(Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare ’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوسَٰى كُوَ يَا رِغَا يَا بَا رَبِنْ ذُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ طَيَ رَبُوانْ غَادُوانْ ڧَسَا عَبَشَنْ؞ غَ سَوْرَنْ رَبِنْ ذُرِيَرْ كُوَ يُواْشُوَ يَبَاسُ رَبُوانْ غَادُوانْ ڧَسَرْ تَرٜىٰدَ یَنْعُوَنْسُ عَيَمَّثِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ يُواْدَنْ؞ سَعَدَّ يُواْشُوَ يَسَلَّمٜىٰسُ، سُكُواْمَ غِدَاجٜىٰنْسُ، يَسَا مُسُ أَلْبَرْكَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,