Joshua 22:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da ’yan’uwanku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ مُسُ «كُكُواْمَ غِدَاجٜىٰنْكُ دَ أَرْزِڧِنْكُ مَيْ يَوَ، تَرٜىٰدَ دَبُّواْبِے مَاسُيَوَ دَ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ دَ تَغُلَّ دَ بَڧِنْ ڧَرْڢٜىٰ دَ كُمَ رِيغُنَ مَاسُيَوَ؞ كُرَبَ دَ یَنْعُوَنْكُ دُكَنْ كَايَنْ دَ كُكَ ݣُوشٜىٰ دَغَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da 'yan'uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.”