Joshua 23:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَنْذُ إِنَ دَبْ دَ بِنْ حَنْيَرْ دَ كُواْوَ عَدُونِيَا يَكَنْبِے؞ كُواْوَنّٜىٰنْكُ يَسَنِ أَ ذُوثِيَارْسَ دَ رَنْسَ ثٜىٰوَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَبَاكُ دُكَنْ أَبُبُوَ مَاسُ ݣَوْ وَطَنْدَ يَيِ مُكُ أَلْڧَوَرِ؞ كُواْوَنٜىٰ أَلْڧَوَرِنْ دَ يَيِ مُكُ يَثِكَ، بَ كُواْ طَيَنْدَ يَكَاسَ ثِكَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.