Joshua 24:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Na kawo ku ƙasar Amoriyawa waɗanda suke gabas da Urdun. Suka yi yaƙi da ku, amma na ba da su a hannunku, na hallaka su a gabanku, kuka kuma mallaki ƙasarsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً نَكَٰوُاْكُ عَڧَسَرْ أَمُواْرِيَاوَا، وَطَنْدَ سُكَ ذَوْنَ أَغَبَشِنْ يُواْدَنْ؞ سُكَ يَاڧٜىٰكُ، عَمَّا نَبَاكُ نَصَرَا عَكَنْسُ؞ نَكُمَ هَلَكَاسُ دَغَ غَبَنْكُ، كُكَ مَلَّكِ ڧَسَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.