Joshua 3:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتُواْثِنْ دَسُكٜىٰ طَوْكٜىٰ دَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ ، عُبَنْغِجِ نَدُكَنْ دُونِيَا، ذَاسُ شِغَ كُواْغِنْ؞ دَظَرَرْ سُكَسَا تَڢِنْ ڧَڢَاڢُنْسُ عَثِكِنْ ضُوً كُواْغِنْ يُواْدَنْ، ضُوً ذَيْ يَنْكٜىٰ، ضُوً دَيَكٜىٰ غَنْغَرُواْوَ عَكُواْغِنْ ذَيْ ڟَيَ يَتَارُ أَوُرِے طَيَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A sa'ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.”