Joshua 3:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ضُوً دَيَكٜىٰ غَنْغَرُواْوَ يَڟَيَ؞ يَتَتَّارُ أَوُرِے طَيَ يَيِ تُدُ دَغَ نٜىٰسَ سُواْسَيْ، أَوَنِ غَرِنْ دَ عَكٜىٰ كِرَا ءَادَمُ كُسَدَ ظَرٜىٰتَنْ؞ ضُوً دَيَكٜىٰ غَنْغَرُواْوَ ذُوَا تٜىٰكُنْ أَرَبَ، وَتُواْ تٜىٰكُنْ غِشِرِ، يَيَنْكٜىٰ غَبَاطَيَ؞ مُتَنٜىٰنْ كُوَ سُكَ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ أَوُرِنْ دَيَكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ يٜىٰرِكُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko.