Joshua 4:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُ أَمْسَ كُغَيَ مُسُ ثٜىٰوَ ضُوً يُواْدَنْ يَيَنْكٜىٰ سَعَدَّ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ يَڧٜىٰتَرٜىٰ يُواْدَنْ؞ وَطَنَّنْ دُوَڟُو كُواْيَوْشٜىٰ ذَاسُ ذَمَ أَبِنْ تُنَاوَا غَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”