Joshua 4:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَبِے عُمَرْنِنْ يُواْشُوَ؞ سُكَ طَوْكِ دُوَڟُو غُواْمَشَا بِيُ دَغَ ڟَكِيَرْ يُواْدَنْ، دُوڟٜىٰ طَيَ دُواْمِنْ كُواْوَثٜىٰ ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَمَرْ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْثِ يُواْشُوَ؞ سُكَ كُوَ ڧٜىٰتَرٜىٰ دَسُو ذُوَا عِنْدَ سُكَيِ ذَنْ‌غُواْ، عَثَنْ سُكَ أَجِيٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Isra'ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su.