Joshua 6:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai samarin waɗanda suka je leƙen asirin suka shiga suka fitar da Rahab, mahaifinta da mahaifiyarta, da ’yan’uwanta da duk abin da yake nata. Suka fitar da iyalinta gaba ɗaya suka sa su a wani wuri, ba a cikin masauƙin Isra’ilawa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَمَارِنْ دَ سُكَ تَڢِے سُكَ لٜىٰڧِ أَسِيرِنْ ڧَسَرْ سُكَ شِغَ، سُكَ ڢِتَرْدَ رَهَبْ تَرٜىٰدَ بَابَنْتَ دَ مَامَرْتَ دَ یَنْعُوَنْتَ دَ كُمَ دُكَنْ دَنْ‌غِنْتَ؞ سُكَ ݣُوشٜىٰسُ دُكَ، سُكَ سَوْكَرْ دَسُو كُسَدَ بَايَنْ ذَنْ‌غُوانْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa.