Joshua 6:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwan nan bai kashe ta ba, ita da iyalinta da duk abin da yake nata, domin ita ta ɓoye mutanen da Yoshuwa ya aika Yeriko don su leƙo asirin ƙasar kuma ta zauna tare da Isra’ilawa har wa yau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يُواْشُوَ يَثٜىٰثِ رَنْ رَهَبْ كَارُوَرْ نَنْ دَ عِيَلِنْتَ دَ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ نَاتَ، سَبُواْدَ تَٻُواْيٜىٰ یَنْ لٜىٰڧٜىٰنْ أَسِيرِنَّنْ بِيُ وَطَنْدَ يُواْشُوَ يَعَيْكٜىٰسُ يٜىٰرِكُواْ؞ رَهَبْ كُوَ تَايِ ذَمَنْتَ عَثِكِنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كُمَ ذُرِيَرْتَ سُنَ ثِكِنْسُ هَرْوَيَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra'ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko.