Joshua 6:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَمَرْ يَدَّ يُواْشُوَ يَعُمَرْتَ، مَاسُ كَايَنْ يَاڧِ دَ كُمَ ڢِرِسْتُواْثِنَّنْ غُدَا بَݣَويْ رِڧٜىٰ دَ ڧَهُواْنِ سُكَ وُثٜىٰ غَبَ، سُنَ بُوسَ ڧَهُواْنِنْسُ، عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ نَ يَهْوٜىٰهْ كُمَ يَنَ بِنْ بَايَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai waɗanda suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su.