Joshua 6:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Masu tsaro da makamai kuma suna gaban firistoci waɗanda suke busa ƙahoni, masu tsaro daga baya kuma suna bin akwatin alkawari, ana ta busa ƙahoni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَاسُ كَايَنْ يَاڧِ كُوَ سُكَ وُثٜىٰ غَبَنْ ڢِرِسْتُواْثِے مَاسُ بُوسَ ڧَهُواْنِ، سَوْرَنْ مَاسُ كَايَنْ يَاڧِ كُمَ سُنَ بِنْ بَايَنْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ؞ عَثِكِنْ دُكَنْ وَنَّنْ لُواْكَثِ أَنَ تَبُوسَ ڧَهُواْنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni.