Joshua 7:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَاشِ! كَكٜىٰٻٜىٰ مُتَنٜىٰ دَ ڟَرْكِے؞ كَڢَطَا مُسُ سُكٜىٰٻٜىٰ كَنْسُ دَ ڟَرْكِے دُواْمِنْ غُواْبٜىٰ؞ غَمَا غَا أَبِنْدَ نِے يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ نَثٜىٰ، ‹يَا إِسْرَٰٓءِيلَ، كُنَ رِڧٜىٰ دَ أَبُبُوَنْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دُواْمِنْ هَلَّكَرْوَ أَڟَكِيَرْكُ؞ بَذَاكُ عِيَ ڟَيَاوَا أَغَبَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْكُ بَ، سَيْ كُنْ كَوَرْدَ وَطَنَّنْ أَبُبُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.