Joshua 7:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُواْشُوَ تَرٜىٰدَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ طَوْكِ عَكَنْ طَنْ ظٜىٰرَ دَ أَظُرْڢَا دَ رِغَا مَيْݣَوْ دَ سَنْدَنْ ظِينَارِيَ، سُكَ كَٰوُاْسُ أَ ݣُورِنْ عَكُوارْ، وَتُواْ ݣُورِنْ عَذَابَ؞ سُكَ كُمَ طَوْكِ یَیَنْسَ مَاتَادَ مَظَا دَ شَانُنْسَ دَ جَاكُنَنْسَ دَ تُمَكِنْسَ دَ تٜىٰنْتِنْسَ دَ كُمَ دُكَنْ سَوْرَنْ أَبُبُوَنْ دَ يَكٜىٰدَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Joshuwa kuwa tare da dukan Isra'ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da 'ya'yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor.