Joshua 8:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoro; kada ka karaya. Ka ɗauki dukan sojojin ku kai wa Ai hari, gama na ba ka nasara a kan sarkin Ai, mutanensa, birninsa da kuma ƙasarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ كُمَ يَثٜىٰ وَ يُواْشُوَ «كَدَ كَجِڟُواْرُواْ كُواْ كَڢِدَّ ذُوثِيَا؞ سَيْ كَطَوْكِ دُكَنْ سُواْجُواْجِ، كَتَاشِ، كَتَڢِے أَيْ كَڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ؞ غَاشِ، نَارِغَا نَا بَادَ سَرْكِنْ أَيْ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْسَ دَ غَرِنْسَ دَ ڧَسَرْسَ أَهَنُّنْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka.