Joshua 8:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da sarkin Ai ya ga haka, shi da duk mutanen birnin suka hanzarta da sassafe don su gamu da Isra’ilawa, su yi yaƙi da su a wani wurin da yake fuskantar Araba. Amma bai san cewa an yi masa kwanto a bayan birnin ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَرْكِنْ أَيْ يَغَ سُواْجُواْجِنْ يُواْشُوَ، يَطَوْكِ مَتَاكِ دَ سَوْرِ؞ شِے دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْسَ سُكَ ڢِتَ ذُوَا وَجٜىٰنْ ݣُورِنْ يُواْدَنْ دُواْمِنْ سُيَاڧِ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَوُرِنْ دَ دَا سُكَيِ يَاڧِ؞ عَمَّا سَرْكِنْ بَيْسَنْ أَݣَويْ یَنْ ݣُونْتُوانْ ٻَوْنَ عَبَايَنْ غَرِنْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A sa'ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra'ilawa, amma bai san akwai 'yan kwanto a bayan birnin ba.