Joshua 8:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Ai suka juya suka ga hayaƙin birninsu yana tashi sama, amma ba yadda za su iya tsira ta ko’ina, gama Isra’ilawan da suke gudu zuwa cikin jeji suka juya suka fara fafarar waɗanda suke fafararsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ أَيْ سُكَ دُوبِے بَايَ، سُكَغَ هَيَاڧِنْ غَرِنْ يَنَ تَاشِ ذُوَا سَمَ؞ بَابُوَتَ حَنْيَ كُمَ وَدَّ ذَاسُ ڟِيرَا، سَبُواْدَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ غُدُ ذُوَا دَاجِ، سُكَ جُويَا دُواْمِنْ سُڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.