Joshua 9:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ سَلْكُنَنْ ضُوً إِنَبِے كُمَ وَطَنْدَ مُكَثِكَ، سَابَبِّے نٜىٰ أَدَا؞ عَمَّا غَاشِ يَنْذُ سُنْ ڢَرْڢَشٜىٰ؞ رِيغُنَنْمُ كُمَ دَا مَا سَابَبِّے نٜىٰ دَ تَاكَلْمَنْمُ سُنْ ڟُوڢَ سَبُواْدَ تَڢِيَ مَيْ نِيسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!”