Joshua 9:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُواْشُوَ كُوَ يَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ سَلَمَ تَرٜىٰدَسُو ثٜىٰوَ ذَيْ بَرْسُ دَ رَيْ؞ شُوغَبَنِّنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا كُمَ سُكَ ضَنْڟٜىٰ مُسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu.