Judges 1:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ta zuga shi yă roƙi mahaifinta fili. Sa’ad da ta sauko daga jakinta, sai Kaleb ya ce mata, “Me zan yi miki?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَتَذُواْ وُرِنْسَ، سَيْ تَظُغَ عُواتْنِيٜىٰلْ يَضُواْڧِ بَابَنْتَ ڢِيلِنْ غُواْنَ؞ عِتَ كُوَ دَ تَسَوْكَ دَغَ كَنْ جَاكِنْتَ، سَيْ كَلٜىٰبْ يَتَمْبَيٜىٰتَ «مٜىٰ كِكٜىٰسُواْ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”