Judges 1:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutanen Yahuda suka tafi tare da ’yan’uwansu mutanen Simeyon suka fāɗa wa Kan’aniyawan da suke zaune cikin Zefat, suka kuwa hallaka birnin gaba ɗaya. Saboda haka aka kira wurin Horma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ تَرٜىٰدَ یَنْعُوَنْسُ مُتَنٜىٰنْ ذُرِيَرْ سِمٜىٰيُوانْ، سُكَ تَڢِے سُكَثِ كَنْعَنِيَاوَنْ دَسُكٜىٰ دَ ذَمَ أَ ظٜىٰڢَتْ دَ يَاڧِ؞ سُكَ كٜىٰٻٜىٰ غَرِنْ دُواْمِنْ هَلَّكَرْوَ، سُكَ هَلَّكَ شِ؞ سَبُواْدَ حَكَنٜىٰ سُكَ ثَنْجَ وَ غَرِنْ سُنَ، سُكَ كِرَا شِ هُوارْمَ، وَتُواْ هَلَّكَرْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.