Judges 1:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ بَسُ كُواْرِ مَذَوْنَنْ بٜىٰتْ شَنْ دَ نَ تَعَنَكْ دَ نَ دُوارْ دَ نَ إِبْلٜىٰيَمْ دَ نَ مٜىٰغِدُّواْ دَ ڧَوْيُكَنْ دَسُكٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَسُوبَ؞ كَنْعَنِيَاوَنْ كُوَ سُكَ نَاثٜىٰ سُذَوْنَ عَثِكِنْ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta'anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan'aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar.