Judges 1:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutane Yahuda suka ce wa mutanen Simeyon “Ku zo tare da mu a yankin da aka ba mu rabon mu don mu yaƙi Kan’aniyawa. Mu ma mu bi ku wurin naku.” Saboda haka mutanen Simeyon suka tafi tare da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَثٜىٰ وَیَنْعُوَنْسُ مُتَنٜىٰنْ ذُرِيَرْ سِمٜىٰيُوانْ «كُذُواْ تَرٜىٰدَمُو ذُوَا ثِكِنْ يَنْكِنْ رَبُوانْ غَادُوانْمُ، دُواْمِنْ مُيَاڧِ كَنْعَنِيَاوَنَّنْ؞ حَكَ مُو مَا ذَامُ تَڢِے تَرٜىٰدَكُو ذُوَا ثِكِنْ يَنْكِنْ رَبُوانْ غَادُوانْكُ؞» ذُرِيَرْ سِمٜىٰيُوانْ كُوَ سُكَ تَڢِے تَرٜىٰدَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.