Judges 11:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ تُورَ یَنْ عَيْكَ ذُوَا وُرِنْ سَرْكِنْ عٜىٰدُوامْ دُواْمِنْ سُضُواْڧٜىٰشِ يَبَرْسُ سُوُثٜىٰ تَڧَسَرْسَ؞ عَمَّا سَرْكِنْ عٜىٰدُوامْ بَيْيَرْدَ مُسُبَ؞ سُكَ كُمَ تُورَ یَنْ عَيْكَ ذُوَا وُرِنْ سَرْكِنْ مُواْوَبْ دُواْمِنْ سُضُواْڧٜىٰشِ يَبَرْسُ سُوُثٜىٰ تَڧَسَرْسَ؞ عَمَّا شِے مَا بَيْيَرْدَ مُسُبَ؞ سَبُواْدَ حَكَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ ذَوْنَ أَ كَدٜىٰشْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra'ilawa suka zauna a Kadesh.