Judges 11:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَاتَرْ غِلٜىٰيَدْ تَكُمَ حَيْڢَ مَسَ وَطَنْسُ یَیَ مَظَا؞ سَعَدَّ یَیَ نَمَاتَرْ نَنْ سُنْيِ غِرْمَ، سَيْ سُكَ كُواْرِ يٜىٰڢْتَادَغَ غِدَنْ؞ سُكَثٜىٰ مَسَ «بَذَاكَثِ غَادُوانْ وَنِ أَبُ نَبَابَنْمُبَ، غَمَا كَيْ طَنْ وَتَ مَثٜىٰ نٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”