Judges 11:38 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ مَتَ «تَڢِے؞» سَيْ يَسَلَّمٜىٰتَ، تَتَڢِے حَرْ وَتَا بِيُ طِنْ؞ عِتَ دَ أَبُواْكَنْتَا كُوَ سُكَ تَڢِے سُكَ هَوْ ثِكِنْ تُدَّيْ، سُكَيِ بَڧِنْ ثِكِنْ دَ ذَاتَمُتُ تَنَ بُدُرْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu.