Judges 12:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِڢْرَيِمْ سُكَيِ شِرِ دَ كَايَنْ يَاڧِنْسُ؞ سُكَ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ ذُوَا ظَڢُوانْ، سُكَثٜىٰ وَ يٜىٰڢْتَا «مٜىٰيَسَا كَڢِتَ يَاڧِ دَ أَمُّواْنَاوَا بَكَ كِرَامُ مُتَڢِے تَرٜىٰبَ؟ تُواْ، ذَامُ ڧُواْنٜىٰكَ دَ غِدَنْكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”