Judges 13:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Manowa ya tashi ya bi matarsa. Da ya zo wurin mutumin, sai ya ce, “Kai ne wanda ka yi magana da matata?” Ya ce, “Ni ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَنُواْوَ يَتَاشِ يَبِے مَاتَرْسَ يَتَڢِے تَرٜىٰدَ عِتَ؞ دَ يَذُواْ وُرِنْ مُتُمِنْ يَثٜىٰمَسَ «كَيْ نٜىٰ مُتُمِنْ دَ يَيِ مَغَنَ دَ مَاتَتَ؟» سَيْ مَلاَىِٕكَنْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «عِ، نِنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?” Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”