Judges 14:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَا يِتَكُوكَا أَغَبَنْسَ حَرْ سَوْرَنْ ݣُونَكِے بَݣَويْ نَبِكٍ؞ عَمَّا أَ رَانَ تَبَݣَويْ طِنْ سَبُواْدَ ڟَنَنِنْ ڢِتِنَرْتَ، سَيْ يَڢَطَا مَتَ مَعَنَرْ كَثِثِ كَثِثِنْ؞ عِتَ كُوَ تَجٜىٰ تَڢَطَا وَمُتَنٜىٰنْتَ ڢِلِسْتِيَاوَا مَعَنَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta kuwa yi ta yi masa kuka har rana ta bakwai ta ƙarewar bikinsu. Amma a rana ta bakwai, ya faɗa mata amsar saboda yawan fitinarta. Ita kuwa ta faɗa wa mutanenta amsar ka-cici-ka-cicin.